Kwamishinan tsaro na cikin gida da ayyuka na musamman na jihar Kano shima ya yi murabus saboda sauya shekan da Gwamna, Abba Kabir Yusuf ya yi daga NNPPP zuwa APC.
Kwamishinan tsaro na cikin gida da ayyuka na musamman na jihar Kano, Ibrahim Umar, ya bi sahun kwamishinonin da ya zuwa yanzu suka ajiye mukamansu biyo bayan sauya sheka da gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf ya yi zuwa jam’iyyar All Progressives Congress.
Kwamishinan ya bayyana hakan ne a cikin wata wasikar murabus da ya aikewa gwamnan jihar Kano, Abba Yusuf, kuma ya saki wa manema labarai a yammacin ranar Litinin.
A cewarsa, matakin ya samo asali ne daga rashin jituwar da ke tsakanin gwamnan jihar Kano da mai ba shi shawara kan harkokin siyasa, Sanata Rabi’u Kwankwaso.
Wasikar ta ci gaba da cewa, “Na rubuto tare da matukar godiya da kuma kwarin guiwa na mika takardar murabus na daga mukamina na kwamishinan tsaro na cikin gida da ayyuka na musamman na jihar Kano, nan take, ina so in mika godiyata ga mai girma gwamna bisa amincewa da amincewar da ka yi min.

0 Comments:
Post a Comment