Kamfanin matatar man fetur na Dangote ta sanar da ƙara farashin naira N100 akan kowace litar mai.
Kamfanin ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin.
A cewar matatar yanzu haka ana siyar da shi akan Naira 799 kan kowace lita ga masu sari, yayin da za'a rika sayar da shi akan Naira 839 a gidajen mai na MRS.
Inda ya tashi daga farashin Naira 699 ga masu sari, da kuma Naira 739 a gidajen mai akan kowace lita da ake sayarwa tun a watan Disambar bara.

0 Comments:
Post a Comment