Dan Kwankwaso ya sanar da yin murabus a matsayin kwamishinan matasa da ci gaban wasanni na jihar Kano.
Mustapha Rabiu Kwankwaso, da ga dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar New Nigeria Peoples Party a 2023, Sanata Rabi'u Kwankwaso, ya yi murabus daga mukaminsa na kwamishinan matasa da ci gaban wasanni na jihar Kano.
Kwankwaso ya sanar da murabus dinsa na zama dan majalisar zartarwa ta jihar a wata sanarwa da ya fitar a shafin sa na Facebook a jiya Litinin.
Ya kuma mika godiyarsa ga Gwamna Abba Yusuf da ya ba shi damar yin aiki a gwamnati.
Sanarwar ta kara da cewa, “A cikin zuciya daya na sanar da murabus na a matsayina na mai girma kwamishinan ma’aikatar matasa da wasanni kuma memba a majalisar zartarwa ta jihar Kano.

0 Comments:
Post a Comment