Dan tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, Abba Atiku, ya bayyana cewa babu wata jam’iyyar siyasa da za ta iya kayar da shugaban kasa Bola Tinubu a zaben 2027.
Abba, wanda ya koma jam’iyyar All Progressives Congress (APC) kwanan nan, yayi magana ne a jiya, a Yola, babban birnin jihar Adamawa, bayan karbar katin shaidar zama mamba a unguwar Gwadabawa dake karamar hukumar Yola ta Arewa.
A cewarsa, ya yanke shawarar komawa jam’iyyar APC ne saboda burinsa na bayar da gudummawa ga “sabuwanta tattalin arziki da ci gaban jama’a”.
Ya ce: “Ina so in bayyana a fili cewa babu wani ko wata jam’iyyar siyasa da za ta hana Shugaba Tinubu komawa Aso Rock a 2027.
"'Yan Najeriya sun ga kyakkyawan aikinsa; shi ba dan kabila ba ne kuma ba ya yin nade-nade bisa addini ko yanki.
Yana yanke shawararsa bisa cancanta ne kawai," in ji shi.
"Shugaban kasa na bukatar goyon bayan mu don ci gaba da aiki mai kyau, ya kamata mu tara mutane fiye da jam'iyya, don marawa shugaban mu baya," in ji shi.
A halin yanzu, Adamu Atiku, babban da ga Atiku kuma yayan Abba Atiku, ya ci gaba da zama a jam’iyyar PDP, kuma a halin yanzu yana rike da mukamin kwamishinan ayyuka da makamashi a karkashin Gwamna Ahmadu Fintiri na jihar Adamawa.
Rahotanni sun bayyana cewa tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar na shirin tsayawa takarar shugabancin kasa a karkashin jam’iyyar African Democratic Congress, ADC, duk da cewa babu daya daga cikin ‘ya’yansa da ke cikin jam’iyyar a halin yanzu.

0 Comments:
Post a Comment