Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da cewa wasu jami’anta sun shirya makarkashiyar yi ma shugaban ƙasa Bola Tinubu juyin mulki.
A watan Oktoban shekarar da ta gabata ne, aka samu rahotannin cewa hukumar leken asiri ta DIA ta kama wasu jami’an soji masu mukamin Kyaftin zuwa Birgediya-Janar, tare da tsare su saboda zarginsu da yunkurin hambarar da gwamnatin shugaba Tinubu.
A wata sanarwa da ya fitar bayan rahoton, Daraktan yada labarai na hukumar tsaron, Samaila Uba, Manjo-Janar, ya tabbatar da cewa kwamitin binciken ya mika rahotonsa ga “hukumar da ta dace”.
Uba ya ce wadanda ke da kararrakin da za su amsa za a gurfanar da su a gaban kwamitin shari’a na soja da ya dace domin fuskantar shari’a kamar yadda dokar rundunar soji da sauran ka’idojin hidima suka tanada.
Ya ce, “Rundunar Sojin Najeriya (AFN) na son sanar da jama’a cewa an kammala bincike kan lamarin kuma an mika rahoton ga hukumomin da suka dace.
“Tsarin binciken da aka gudanar bisa ka’idojin soji da aka kafa, ya yi nazari sosai kan duk wani yanayi da ya dabaibaye ma’aikatan da abin ya shafa.

0 Comments:
Post a Comment