Kwamishinan kimiya da fasaha na jihar Kano ya yi murabus Saboda ikirarin da ya yi cewa gwamnatin jihar ta kauce ma akidar da aka zabe ta a kai.
Kwamishinan kimiya da fasaha da kirkire-kirkire na jihar Kano, Hon. Yusuf Kofarmata, ya yi murabus daga mukaminsa na mamba a majalisar zartarwa ta jihar, saboda abin da ya bayyana a matsayin kaucewa akidar siyasar da ta kai gwamnati mai ci a matsayin da ta ke.
Kofarmata ya sanar da murabus din nasa ne a wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadin da ta gabata, inda ya ce an dauki matakin ne bisa gaskiya da kuma sahihin ja-goranci.
“Na ajiye mukamina na kwamishina kuma mamba a majalisar zartarwa ta Jihar Kano, ba zan iya ci gaba da aiki a karkashin gwamnatin da ta kaucewa akidar da ta kawo ta mulki ba,” inji shi.
Tsohon kwamishinan, wanda ya yi aiki a ma’aikatar ilimi mai zurfi da kuma ma’aikatar kimiyya da fasaha da kirkire-kirkire, ya gode wa shugabannin jam’iyyar NNPP da kuma manyan jiga-jigan siyasa kan damar da ya samu wajen hidimta ma Jihar.

0 Comments:
Post a Comment