An soke lasisin aikin jinya na wata 'yar asalin Najeriya saboda yin barci a lokacin aiki a ƙasar Australia

An soke lasisin aikin jinya na wata 'yar asalin Najeriya saboda yin barci a lokacin aiki a ƙasar Australia

Wata ma’aikaciyar jinya 'yar asalin Najeriya ta rasa lasisi aikinta a Ƙasar Australia saboda yawan yin barci a bakin aiki.

An soke lasisin aikin wata ma’aikaciyar jinya ‘yar asalin Najeriya, haifaffiyar ƙasar Australia bayan da wata kotu ta gano cewa tana yin barci akai-akai a yayin da take bakin aikin dare a wani wurin kula da tsofaffi a babban birnin ƙasar, Sydney.

Chimzuruoke Okembunachi, mai shekaru 25, an soke rajistar aikin jinyanta tare da cire sunanta daga rajistar bayan da Kotun Hukunta masu aiki ta NSW ta yanke hukuncin cewa abin da ta yi ya kasance na rashin da'a ne da kuma nuna rashin kwarewa.

SHARE THIS

Author:

I am a blogger by passion and a Website developer by profession, I am currently the CEO of Hausalive.com.ng, a website that brings you a daily needful and useful contents.

0 Comments: