Ana gudanar da zabe zagaye na uku Kuma na karshe a ƙasar Myanmar

Ana gudanar da zabe zagaye na uku Kuma na karshe a ƙasar Myanmar

Ƙasar Myanmar na gudanar da zagayen karshe na zaben ƙasar, yayin da jam'iyyar da sojoji masu mulkin ƙasar ke marawa baya ke kan gaba wajen samun gagarumin nasara.

An bude rumfunan zabe a kasar Myanmar a zagaye na uku kuma na karshe na zaben gama gari mai cike da cece-kuce, inda jam'iyyar da ke samun goyon bayan sojoji ke shirin samun gagarumin rinjaye.

An fara kada kuri'a a garuruwa 60, ciki har da biranen Yangon da Mandalay, da karfe shida na safe agogon kasar a ranar Lahadi.

Sai dai tun kafin kammala zagayen karshe na zaben, wani Jami’in Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana zaben a matsayin ‘haramtacce’, yayin da kungiyar ASEAN ta ce ba za ta tabbatar da zaben ba.

Masu sukar zaben dai sun ce bashi da inganci, kuma an yi shi ne domin halasta mulkin soja a Myanmar, kusan shekaru biyar bayan hambarar da zababbiyar gwamnatin Aung San Suu Kyi, wanda ya kai ga yakin basasa da ya yi sanadin mutuwar dubban mutane tare da raba sama da mutane miliyan 3.5 da muhallansu.

Har yanzu a na ci gaba da tsare Aung San Suu Kyi, kuma kamar sauran kungiyoyin adawa da dama, an wargaza jam'iyyarta ta National League for Democracy (NLD), tare karkata fagen siyasan kasar wajen goyon bayan jam'iyyar Union Solidarity and Development Party (USDP) mai samun goyon bayan sojin ƙasar, wadda ke kan gaba a zaben.

Ya zuwa yanzu dai jam'iyyar USDP ta samu kujeru 193 daga cikin 209 na majalisar wakilai, da kuma kujeru 52 daga cikin 78 na majalisar dattawa, a cewar hukumar zaben kasar.

Hakan na nufin cewa tare da kujeru 166 da aka tanadarwa sojoji, suna da jumullar kujeru sama da 400 daga cikin 294 da ake bukata kafin samun damar kafa Gwamnati.

Post a Comment

Please Select Embedded Mode To Show The Comment System.*

Previous Post Next Post

Contact Form