Kylian Mbappe ya zura kwallaye biyu a wasan da Real Madrid ta doke Villarreal da ci 2-0 wanda hakan yaba kungiyarsa daman darewa teburin gasar ta Laliga.
Nasaran yasa Real ta koma tazarar maki biyu tsakaninta da Barcelona, wacce za ta karbi bakuncin Real Oviedo a ranar Lahadi.
Zuwa yanzu Mbappe ne ke Kan gaba wajen zura kwallaye a gasar inda ya ci kwallaye 21 a kakar wasa ta bana.
Real ta samu ta samu nasara a wasanninta uku a jere karkashin sabon kociyanta, Arbeloa , kuma nasaran da ta samu akan Villarreal na iya zama muhimmin mataki na farfado da himmar Kungiyar a bana.
Tags
Labaran Wasanni
_1.jpeg)