'Yan sanda sun kama wata amarya saboda zargin ta kashe Angonta da gubar bera a Jigawa.
Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta damke wata Amarya bisa zargin sanya wa mijinta guba, wanda ya mutu bayan cin abinci.
Lamarin ya faru ne a ranar 23 ga Janairu, 2026, da misalin karfe 5pm na yamma a kauyen Gauza da ke karamar hukumar Jahun a jihar Jigawa.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin a cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a Dutse, babban birnin jihar a yau Asabar, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa, SP Shi’isu Adam, ya ce marigayin ya ci abincin rana a gida kafin kwatsam ya kamu da rashin lafiya.
A cewar mai magana da yawun ‘yan sandan, an garzaya da mutumin asibiti domin kula da lafiyarsa amma ya mutu a lokacin da yake karbar kulawa.
Bayan afkuwar lamarin ne jami’an tsaro na sashen Jahun suka kai dauki inda suka damke matar marigayin a matsayin babban wanda ake zargi.
SP Shi’isu Adam ya ce “a yayin da ake yi mata tambayoyi, wadda ake zargin ta amsa laifin sa guba (shinkafar bera) a abincin.”
Ya kara da cewa "wanda ake zargin ta yi ikirarin cewa ta aiki dan uwanta ne ya sayo gubar bera da aka yi amfani da shi wajen aikata wannan aika aikar."
Tags
Labarai
