Jagoran Jam'iyyar NNPP na kasa, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso, ya ayyana ranar 23 ga watan Janairu a matsayin ranar cin amana ta duniya.
Ya baiyana haka be a lokacin da yake jawabi ga magoya bayansa a gidansa da ke Miller Road da ke Kano, Kwankwaso ya yi tsokaci game da ranar, inda ya ce ra’ayin daukar ranar a haka ya samo asali ne daga masu sharhi a shafukan sada zumunta wadanda suka bayyana ficewar gwamnan Kano daga Jam'iyyar NNPP a matsayin cin amana.
Ya ce, “Babu wanda ya dauki hankalina fiye da wanda ya buga sharhin, da ke nuna cewa mu ayyana ranar 23 ga watan Janairu a matsayin ranar cin amana ta duniya".
"Saboda haka, a matsayina na jagora kuma jigo na wannan tafiya, ina bayyana cewa na goyi bayan sanarwar," in ji shi.
Kwankwaso ya kara da cewa daga yanzu za a rinka gudanar da bukukuwa na musamman domin tunatar da 'yan uwa abubuwan da suka faru a wannan ranar.
Gwamna Abba Kabir Yusuf, wanda ake kyautata zaton komawarsa Jam'iyyar (APC), ya bayyana ficewarsa daga jam’iyyar NNPP, a ranar 23 ga watan Janairu, 2026.
Inda ya baiyana matsalolin da Jam'iyyar ke fama da shi wanda yaki ci yaki cinyewa a matsayin dalilan ficewarsa.
