Gwamnatin tarayya ta amince da gina layin dogo na Naira Tiriliyan 1 ga jihar Kano, a wani mataki da ake sa ran zai kawo sauyi ga harkokin sufurin birane da habaka tattalin arzikin jihar.
Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ne ya bayyana amincewar yayin da yake jawabi ga ‘yan tawagar Kano da suka halarci gasar karatun Alkur’ani ta kasa da aka gudanar a jihar Borno a shekarar 2025.
Sanarwar hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, a ranar Laraba.
A cewar gwamnan, aikin layin dogo an yi shi ne domin samar da tsarin zirga-zirgar jama’a na zamani, mai inganci da araha wanda zai hada muhimman gundumomi a cikin babban birnin Kano, da saukaka cunkoson ababen hawa da inganta zirga-zirgar jama’a.
Gwamna Yusuf ya ce aikin ya nuna yadda gwamnatinsa ta samu daidaito a siyasance a baya-bayan nan da gwamnatin tarayya karkashin jam’iyyar APC, inda ya ce an dauki matakin ne saboda bukatar jawo muhimman ayyukan raya kasa zuwa Kano.

0 Comments:
Post a Comment