Iran ta ce a shirye take ta mayar da martani fiye da wanda tayi a baya matukar Amurka ta kai mata hari.

Iran ta ce a shirye take ta mayar da martani fiye da wanda tayi a baya matukar Amurka ta kai mata hari.

Iran ta ce a shirye take ta mayar da martani fiye da wanda tayi a baya matukar Amurka ta kai mata hari.

Hukumomin Iran sun yi ishara da cewa a shirye suke su kare kasarsu a daidai lokacin da Amurka ke ci gaba da barazanar kai harin soji, tare da kokarin da kasashen yankin Larabawa ke yi na kaucewa wani sabon rikici a yakin gabas ta tsakiya.

Yunkurin diflomasiyya yana ƙaruwa yayin da Iran ke jaddada shirye-shiryen tsaro kan tattaunawa da Amurka.

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Iran Esmaeil Baghaei ya bayyana cewa, ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araghchi zai gudanar da babban taro a kasar Turkiyya ranar Juma'a.

Baghaei ya kara da cewa Tehran na neman "karfafa huldar da ke tsakaninta da makwabta bisa moriyar juna".

Ziyarar ta zo ne a daidai lokacin da ake ta tattaunawa mai zurfi, a daidai lokacin da shugabannin yankin ke fatan shawo kan Amurkar da kada a kai wa Iran hari, sannan kuma bangarorin biyu su sami wata matsaya.

Sai dai Jirgin yakin ruwan Amurka mai suna Armanda - kamar yadda Shugaba Donald Trump ya kira shi - ya isa kusa da gaban ruwan Iran, karkashin jagorancin jirgin saman USS Abraham Lincoln.


SHARE THIS

Author:

I am a blogger by passion and a Website developer by profession, I am currently the CEO of Hausalive.com.ng, a website that brings you a daily needful and useful contents.

0 Comments: