Wani jirgin sama dauke da mutane 15 da suka hada da dan majalisar dokokin Colombia Diogenes Quintero ya yi hadari a wani yanki mai tsaunuka kusa da kan iyakar Venezuela a ranar 28 ga watan Janairu.
Kamfanin dillancin labaran AFP ya bayar da rahoton cewa, jirgin ya taso ne daga birnin Cúcuta da ke kan iyakar kasar, kuma ya samu tangardan sadarwa ne tsakanin matukan da dakin taimakon masu kula da zirga-zirgar jiragen sama jim kadan kafin a shirya saukarsa a garin Ocaña da ke kusa da shi da misalin karfe 5:00 na yamma.
"Babu wanda ya tsira daga hadarin," kamar yadda wani jami'in hukumar kula da sufurin jiragen sama ya shaidawa AFP.
Jirgin na dauke ne da fasinjoji 13 da ma'aikatansa biyu.
_2.jpeg)
0 Comments:
Post a Comment