Gwamnan Ebonyi ya kori kwamishina da sarakunan gargajiya bisa rikicin kabilanci da ya haifar da kashe-kashe a ƙaramar Hukumar Afikpo.

Gwamnan Ebonyi ya kori kwamishina da sarakunan gargajiya bisa rikicin kabilanci

Gwamnan Ebonyi ya kori kwamishina da sarakunan gargajiya bisa rikicin kabilanci da ya haifar da kashe-kashe a ƙaramar Hukumar Afikpo.

Gwamnan jihar Ebonyi, Francis Nwifuru, ya bayar da umarnin korar sarakunan gargajiya na kabilar Amasiri na karamar hukumar Afikpo tare da bayar da umarnin janye ma’aikatansu.

Ya kuma kori kwamishinan ilimin manyan makarantu na yankin Farfesa Amari Omaka, tare da rusa dukkanin tsarin shugabancin al’umma na siyasa da na gargajiya.

Wannan matakin ya biyo bayan wani mummunan hari da aka kai kan Okporojo a unguwar Oso Edda da ke karamar hukumar Edda, inda aka yi zargin fille kawunan mutane hudu, tare da dauke kawunansu da wasu ‘yan kabilar Amasiri suka yi.

Gwamnan ya ba da umarnin ne a ranar Asabar din da ta gabata yayin wata ziyarar tantancewa da ya kai garin Okporojo, inda ya yi jawabi ga mazauna garin, shugabannin al’umma, hukumomin tsaro da jami’an gwamnati.

Nwifuru ya bayyana harin a matsayin "abin takaici" kuma ya ce bai kamata a amince da irin wannan ta'asa ba a jihar Ebonyi.

Ya kuma ba da tabbacin cewa gwamnatin jihar za ta dauki matakin tunkarar wadanda suka aikata wannan aika-aika, yana mai jaddada cewa rayukan da aka rasa ba za su kasance a banza ba.

Ya bukaci mazauna yankin da su kwantar da hankula su rungumi zaman lafiya, yana mai gargadin cewa duk wani nau’in ramuwar gayya zai kara dagula lamarin. A cewarsa, ayyukan gwamnati za su kasance masu tsayin daka amma bisa ga bukatar hana ci gaba da barkewar rikicin.

Nwifuru ya bayyana cewa rikicin ya dau tsawon shekaru duk da kokarin sasantawa da dama da suka hada da yarjejeniyar kan iyaka tsakanin al’ummomin da abin ya shafa, yana mai korafin cewa an saba karya irin wadannan yarjejeniyoyin.

Ya lura cewa ziyarar tasa wata alama ce mai karfi da ke nuna cewa jihar ba za ta kara amincewa da rashin bin doka da oda ba.

Da ya koma kan rawar da al’ummar Amasiri ke takawa a rikicin, gwamnan ya yi wani kakkausan gargadi, inda ya bayyana cewa tashin hankali ba zai taba kai ga cimma matsaya mai ma’ana ba.

Sakamakon haka, Nwifuru ya sanar da rusa kungiyar raya garin Amasiri da mambobinta na zartaswa, tare da janye takardar shedar sarkin gargajiya, tare da korar duk wasu hakimai na kauyen Amasiri mai cin gashin kansa.

Ya kuma ba da umarnin korar duk wasu masu rike da mukaman siyasa daga al’ummar Amasiri tun daga mambobin kwamitin gudanarwa har zuwa kwamishinoni da ke aiki a gwamnatinsa.

Da yake jaddada kudirin gwamnatinsa na maido da dawwamammen zaman lafiya a karamar hukumar Edda, gwamnan ya yi alkawarin cewa al’umma za su fara samun ci gaba ta fuskar gwamnati nan da shekara mai zuwa.

SHARE THIS

Author:

I am a blogger by passion and a Website developer by profession, I am currently the CEO of Hausalive.com.ng, a website that brings you a daily needful and useful contents.

0 Comments: