Shugaba Bola Tinubu ya dawo Najeriya daga ziyarar aiki da ya kai kasar Turkiyya inda ya kulla yarjejeniyoyi har guda tara da shugaba Erdoğan.
Jirgin Airbus A330 dake jigilar shugaban ya isa filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe dake Abuja da misalin karfe 8:55pm na dare ayau Asabar.
An tabbatar da zuwan Tinubu a wata sanarwa da fadar shugaban kasa ta fitar ga manema labarai a daren yau Asabar.
Ziyarar wacce aka fara a ranar Talatar da ta gabata, shugaba Tinubu ya tattauna da shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan tare da sa ido kan yadda aka rattaba hannu kan yarjejeniyoyi tara da suka shafi tsaro da makamashi da tsaro da bincike da sauran manyan tsare-tsare.
_5.jpeg)
0 Comments:
Post a Comment