Akalla Falasdinawa 31 da suka hada da kananan yara shida ne aka kashe a hare-haren da Isra’ila ta kai zirin Gaza da Khan Younis tun daga wayewar garin yau, ciki har da akalla bakwai da suka mutu a wani harin bam da aka kai a hedkwatar 'yan sanda a unguwar Sheikh Radwan, kamar yadda majiyoyin lafiya suka shaida wa Kafar talabijin na Al Jazeera.
Harin dai ya zo ne kwana guda kafin Isra'ila ta sake bude mashigar Rafah da ke hade Gaza da Masar a ranar Lahadi a karon farko tun watan Mayun 2024.
Ofishin yada labarai na gwamnatin Gaza ya ce sama da Falasdinawa 500 ne sojojin Isra'ila suka kashe tun bayan da yarjejeniyar tsagaita bude wuta da Amurka ta kulla a Gaza ta fara aiki a ranar 10 ga watan Oktoba.

0 Comments:
Post a Comment