Babban alkalin kasar Iran ya gargadi masu zanga-zangar wadandada suka fito kan tituna a lokacin da ake fama da rikicin tattalin arziki, cewa ba za a yi sassauci ga wadanda ke taimakawa abokan gaba akan cutar da Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba, yana mai zargin Amurka da Isra'ila da Kara ingiza hargitsi a kasar.
"Bayan sanarwar da Isra'ila da shugaban Amurka suka yi, babu wani uzuri ga masu zuwa kan tituna domin tarzoma da tashe-tashen hankula," in ji babban mai shari'a Gholamhossein Mohseni Ejei da yake jawabi a ranar Laraba a wani sharhi kan zanga-zangar da kamfanin dillancin labarai na Fars ya gabatar.
A yayin da ake ci gaba da tashe tashen hankula, Iran na fuskantar matsin lamba daga kasashen duniya bayan da shugaban Amurka Donald Trump ya yi barazanar a makon da ya gabata cewa idan Tehran ta kashe masu zanga-zangar lumana da karfi, wanda al'adarsu ce, Amurka za ta kawo musu dauki.
Barazanar nasa - tare da jadadda cewa Amurka tana "kulle kuma a shirye take ta tafi" - ta zo ne watanni bakwai bayan da sojojin Isra'ila da na Amurka suka kai hare-hare kan wuraren nukiliyar Iran a yakin kwanaki 12.
Bugu da kari, Firayim Ministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya goyi bayan masu zanga-zangar a ranar Lahadin da ta gabata, yana mai gaya wa ministocin, "Abu ne mai yiyuwa mu kasance a daidai lokacin da al'ummar Iran ke daukar makomarsu a hannunsu."

0 Comments:
Post a Comment