Amurka zata fice daga kwamitoci da Kungiyoyin Majalisar Dinkin Duniya guda 66, wadanda su ka saba wa muradun Amurka, inji Donald Trump.
Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da cewa yana shirin janye Amurka daga kungiyoyin Majalisar Dinkin Duniya 66, ciki har da manyan kwamitocin hadin gwiwa kan sauyin yanayi, zaman lafiya da demokradiyya.
A cikin wata takardar shedar shugaban kasa da fadar White House ta raba wa manema labarai a ranar Laraba da yamma, Trump ya ce matakin ya biyo bayan nazarin da aka yi ne game da "kungiyoyi da kwamitoci da yarjejeniyoyin da suka saba wa muradun Amurka".

0 Comments:
Post a Comment