Kwamitin Shura na Jihar Kano, ya ta dakatar da Lawan Shuaibu Triumph daga yin wa’azi har zuwa lokacin da zai kammala bincike game da zarginsa da ake yi da yin batanci ga Janibin Annabi Muhammad (S.A.W).
Sakataren kwamitin, Alhaji Shehu Wada Sagagi ne, ya bayyana hakan a taron manema labarai da aka gudanar a yau Laraba.
Kamar yadda Sakataren kwamitin ya sanar, ya baiyana cewan bayan gudanar da bincike mai zurfi da kwamitin ya yayi, an rubuta zarge-zargen da aka tabbatar suna da hujja domin gabatar da su ga Wandan ake zargin domin ya kare kansa.
Kwamitin ya kara da cewa za a tura masa da takardar gaiyata domin ya zo ya kare kansa, kafin daga bisani a aika da shawarwari ga gwamnati don daukar mataki.
Idan ba'a manta ba a makon da ya gabata ne aka nuna yadda wasu matasa cikin fushi suka yi dandazo a gidan gwamnatin jihar Kano, inda suke rokon gwamnatin da ta dauki mataki a kan Malam Lawal Triumph saboda zarginsa da su ke yi da yin kalaman batanci ga shugaban Halitta ANNABI MUHAMMAD Sallallahu Alaihiwasallam a lokacin da yake gudanar da karatu.
Inda daga bisani gwamnan jihar Kano Injiniya Alh Kabir Yusuf ya saurari kokensu ya Kuma bukaci da su gabatar da koken nasu a rubuce.
_2.jpeg)
0 Comments:
Post a Comment