Jami'an tsaro sun kama wasu ‘yan sandan bogi guda biyu dauke da tabar wiwi a Taraba

Jami'an tsaro sun kama wasu ‘yan sandan bogi guda biyu dauke da tabar wiwi a Taraba.

Dakarun rundunan soji ta 6 tare da hadin gwiwar jami’an hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA a jihar Taraba sun kama wasu jami’an ‘yan sandan bogi su biyu dauke da kayan wiwi a cikin motoci biyu.

Wata sanarwa da mukaddashin Daraktan hulda da jama’a na rundunar soji ta 6, Laftanar Umar Muhammad, ya fitar a ranar Laraba, ya ce an kama mutanen ne a Wukari.

Wadanda ake zargin suna sanye da kakin ‘yan sanda, an same su da wasu motoci kirar Toyota Hilux guda biyu dauke da abubuwan da ake zargin tabar wiwi ce.

“Bincike na farko ya nuna cewa babu daya daga cikin mutanen da ke yiwa hukumar ‘yan sandan aiki.

“Motocin dauke da tabar wiwi an gano cewa an yi lodin su ne daga Akure, jihar Ondo, kuma sun nufi jihar Adamawa ne kafin su shiga hannun hukuma.”



SHARE THIS

Author:

I am a blogger by passion and a Website developer by profession, I am currently the CEO of Hausalive.com.ng, a website that brings you a daily needful and useful contents.

0 Comments: