Sojojin Isra'ila sun kama wasu daga cikin masu fafutuka dake cikin jiragen ruwa da ake Kira da Global Sumud Flotilla da ke kan hanyar zuwa zirin Gaza domin kai kayan agaji ga Al'ummar Falastinawa dake cikin ukubar Israi'la.
Masu fafutukan sun tashi ne daga Kasashen Sifaniya da itali inda suka kudiri aniyar kai kayan agaji zuwa zirin na Gaza duk rintsi duk wuya.
Ko a cikin watan satumba sai da aka samu rahoton cewa Israi'la ta kai masu hari da jiragen sama marasa matuka a kusa da iyakan Tunisia Amma duk da haka basu yi kasa a gwiwa ba.
Tun a baya daman Isra'ila ta lashi takobin dakatar da jiragen ruwa da ke kan hanyar zuwa Gaza tana mai da'awar cewa masu aikin sa kai din na kokarin "keta dokar hana zirga-zirgar jiragen ruwa", amma dokar kasa da kasa ta fito karara kan bayar da damar Kai agajin jin kai zuwa kowace kasa.
0 Comments:
Post a Comment