Amurka ta haramta wa tawagar Hukumar kwallon kafar kasar Iran shiga kasar domin halartan bikin kaddamar da jadawalin gasar cin kofin duniya da za ayi kasar a 2026, a cewar kakakin hukumar kwallon kafa ta Iran (FFI), Amir-Mehdi Alawi.
Daga cikin wadanda abin ya shafa har da shugaban FFI Mehdi Taj, da babban koci Amir Ghalenoei, da kuma wasu jami'an hukumar guda bakwai, in ji kakakin, kamar yadda jaridar Shargh ta ruwaito.
Yanzu dai hukumar ta FFI na fatan shawo kan shugaban hukumar ta FIFA Gianni Infantino ya janye matakin.
Kakakin ya yi tunanin Infantino zai dage haramcin nan da makonni biyu masu zuwa.
A ranar 5 ga watan Disamba ne za a yi jadawalin gasar cin kofin duniya na 2026 a birnin Washington.
Tun a baya an nuna damuwa game da dokar hana shige da fice da shugaban Amurka Donald Trump ya sanya wa Iraniyawa saboda takun saka da ke tsakanin Kasashe biyu.
0 Comments:
Post a Comment