A yau Juma'a ne Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya sanar da wata gagarumar garanbawul a shugabancin rundunar sojin kasar a wani bangare na kokarin karfafa rundunar tsaron kasar Najeriya.
A sanarwa da mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai da sadarwa Sunday Dare ya fitar ranar Juma’a, yace an nada Janar Olufemi Oluyede a matsayin sabon babban hafsan tsaron kasar, inda ya maye gurbin Janar Christopher Musa.
Ga jerin sabbin Shugabannin da waɗanda suka maye gurbinsu:
1. Babban Hafsan Tsaro: Laftanar Janar Olufemi Oluyede, wanda ya karbi ragamar mulki daga hannun Janar Christopher Musa.
2. Babban Hafsan Soji: Manjo-Janar W. Shaibu, ya maye gurbin Laftanar Janar Olufemi Oluyede.
3. Babban Hafsan Sojan Sama: Air Vice Marshal S.K. Aneke, wanda ya gaji AVM H.B. Abubakar.
4. Babban Hafsan Sojin Ruwa: Rear Admiral I. Abbas, ya karbi ragamar mulki daga Rear Admiral E. A. Ogalla.
5. Shugaban hukumar leken asiri na tsaro: Manjo-Janar E.A.P. Undiendeye, wanda ke rike da mukaminsa.
Wannan sauyi dai na daga cikin kokarin da shugaba Bola Tinubu yayi na karfafa tsarin tsaron kasa na Najeriya.

0 Comments:
Post a Comment