Majalisar Dinkin Duniya ta sake kakabawa Iran takunkumi

Majalisar Dinkin Duniya ta sake  kakabawa Iran takunkumi

Majalisar Dinkin Duniya ta sake  kakabawa Iran takunkumi a karon farko cikin shekaru goma, bayan da aka kasa cimma matsaya kan batun nukiliyarta da kasashen yammacin duniya.

Takunkumin na zuwa ne watanni uku bayan da Isra'ila da Amurka suka kai wa Iran hari kan cibiyoyin makaman nukiliyarta. 
Tukunkumin sun hada da hana duk wata huldar da ke da alaka da shirin nukiliyar na Teheran da makami mai linzami, kuma ana sa ran zai yi tasiri sosai kan tattalin arzikinta.

Jami'an diflomasiyyar Turai da na Amurka sun jaddada cewa sake kakaba mata takunkumin da akayi somin tabi ne.

Haka zalika Sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio ya bukaci Tehran da ta “karbi tattaunawar kai tsaye, da aka yi cikin aminci.”

Ya kuma yi kira ga kasashe mambobin Majalisar Dinkin Duniya da su gaggauta aiwatar da takunkumi don matsawa shugabannin Iran lamba su yi abin da ya dace ga al'ummarsu, da kuma samun maslaha ga tsaron duniya.

SHARE THIS

Author:

I am a blogger by passion and a Website developer by profession, I am currently the CEO of Hausalive.com.ng, a website that brings you a daily needful and useful contents.

0 Comments: