An yanke wa tsohon ministan noma hukuncin kisa a China saboda samun shi da laifin karban rashawa.

An yanke wa tsohon ministan noma hukuncin kisa a China saboda samun shi da laifin karban rashawa.

Wata kotu a China ta yanke wa tsohon ministan noma hukuncin kisa saboda samun shi da laifin karban rashawa.

Wata sanarwa da kotun ta fitar ta ce, an yanke wa tsohon ministan noma na kasar china hukuncin kisa a ranar Lahadi kan zargin cin hanci da rashawa, tare da jinkirin zartarwa na tsawon shekaru biyu.

Tang Renjian ya karbi tsabar kudi da cin hancin kadarorin da ya kai fiye da yuan miliyan 268 (kwatankwacin naira biliyan 56) tsakanin shekarar 2007 zuwa 2024, in ji kotun jama'ar Changchun da ke lardin Jilin a arewa maso gabashin kasar.

Kotun ta yanke hukuncin cewa cin hancin “ya haifar da babbar asara musamman ga muradun jihar da jama’a, don haka ya bada damar yanke hukuncin kisa a kanshi”, ta kara da cewa Tang ya amsa laifinsa tare da nuna nadama.

Hukuncin Tang shi ne na baya-bayan nan a matakan da shugaba china shugaba Xi Jinping ke dauka don yaki da cin hanci da rashawa wanda ya shafi wasu manyan mutane a kasar.


SHARE THIS

Author:

I am a blogger by passion and a Website developer by profession, I am currently the CEO of Hausalive.com.ng, a website that brings you a daily needful and useful contents.

0 Comments: