Arsenal da Manchester City sun raba maki a wasan da suka buga 1-1 a filin wasa na Emirate dake birnin Landan.
Dan wasan gaban city Erling Haaland ne ya fara zura kwallon farko a ragar Arsenal mintuna 9 kacal da fara wasan, sai dai ana saura mintuna 3 kacal a tashi wasan a minti na 90+3 Gabriel Martinelli ya farke wa Arsenal kwallon inda aka tashi kunnen doki 1-1.
Yanzu Arsenal na mataki na 2 a teburin na premier league da maki 10 yayin da Manchester City ke mataki na 9 da maki 7 sai Liverpool dake Jan ragamar teburin mai maki 15.
0 Comments:
Post a Comment