Shugaban kungiyar kwallon kafar PSG Nasser Al-Khelaifi ya ba dukkan ma'aikatan kungiyar su 600 tikiti kyauta domin tafiya zuwa kallon wasan karshe na gasar cin kofin zakarun nahiyar Turai na UEFA Champions League Wanda za'a buga tsakanin kungiyar kwallon kafar PSG da Inter Milan a filin wasa na Alianz arena dake birnin Munich na kasar Jamus a ranar Asabar 31 ga wannan watan na mayu🏆
Za Kuma su sami karin wasu kyaututtukan idan kungiyar ta lashe gasar 🏆🏅
A ranar laraba ne kungiyar kwallon PSG ta samu nasaran kaiwa wasan karshe na gasar zakarun nahiyar Turai bayan ta doke Arsenal da ci 2-0 a Paris da Kuma 1-0 a London, PSG ta dade tana burin lashe gasar a karon farko a Tarihi Inda a shekarun baya Shugaban kungiyar vvbv ya rinka kashe miliyoyin daloli wajen sayo Manyan 'yan wasa kamar su Mbappe da Neymar da Lionel Messi da Sergio Ramos domin lashe gasar amma hakan bai Samu ba.
Zasu fafata da inter Milan wacce ta taba lashe gasar sau uku a Tarihi kuma tun 2010 rabon da ta sake lashe gasar.
.
.
Article Translation in English Language
PSG president Nasser Al-Khelaifi has given all 600 club employees free tickets to watch the UEFA Champions League final match between PSG and Inter Milan at the Allianz Arena in Munich, Germany on Saturday, May 31.
They will also get more prizes if the team wins the competition 🏆🏅
On Wednesday, PSG reached the finals of the European Champions League after beating Arsenal 2-0 in Paris and 1-0 in London.
PSG has long been hoping to win the competition for the first time in history. In recent years, the president of the club, Nasser Al-Khelaifi, has spent millions of dollars to buy big players such as Mbappe, Neymar, Lionel Messi and Sergio Ramos to win the competition, but that did not happen.
They will compete with Inter Milan, who have won the competition three times in history, and since 2010 when they have won the last competition.

0 Comments:
Post a Comment