Za'a yi fafatawan El Clasico yau tsakanin Barcelona da Real Madrid a Filin wasa na Comp Nou.
Fafatawan dai zata yi zafi kwarai ganin yadda kowace kungiya ke kokarin ganin ta lashe gasar Laliga ta bana.
Barcelona ce dai ke matakin farko a teburin Laligan da maki 79 da kwallaye 58 yayin da Real Madrid din ke biye mata da maki 75 da kwallaye 36, yayin da ya rage wasanni hudu a kacal a kammala gasar ta bana.
A wannan shekaran dai sun fafata har sau uku a tsakaninsu Kuma duk Barcelona ce take samun damar doke Real Madrid din a dukkan karawar.
A Tarihi dai kungiyoyin sun fafata a tsakaninsu har sau 260, yayin da Real Madrid ta doke Barcelona sau 105, Sai Barcelona ta doke Real Madrid din sau 103 yayin da Suka buga canjaras sau 52.
Karawar da Suka yi ta karke a tsakaninsu shine a wasan karshe na lashe gasar Copa del Ray Inda Barcelonan ta samu nasaran akan Real Madrid din da ci 3-2.
Hausawa dai na cewa ba'a san maci tuwo ba sai Miya ta kare.
0 Comments:
Post a Comment