Wasu daga cikin Sunayen unguwannin Zaria da tarihinsu

 

Wasu daga cikin Sunayen unguwannin Zaria da tarihinsu

WASU DAGA CIKIN SUNAYEN UNGUWANNIN ZARIA DA TARIHINSU
1. Anguwar Zaria
   Nan ne inda birnin zaria yake a yanzu.
Ance asalin sa fili ne babu kowa a wurin. Amma a lokacin da ake gina ganuwar birni zamanin Sarki Bakwa Turunku, sai wata ɗiyar sarki da ake kira Zaria tazo taga wannan wuri, daga nan sai ta nemi mutanen daular Zazzau da akace a lokacin cibiyar su na Turunku su dawo wannan wuri domin bada dama ga magina su kammala ginin fadar Sarki, da ganuwa, da rijiyoyi da kuma gidanta a Unguwar Magajiya.
   Don haka ake ganin tun abaya wurin ya zama cibiyar daular na wani lokaci, amma ana kammalawa sai duk suka tashi izuwa sabon waje.
   Tun daga nan kuma sai zaria ya zamo tsirarun mutane kaɗai ke rayuwa a wurin har zuwa karni na goma sha takwas da wajen ya haɓaka izuwa birnin zaria.
  2. Unguwar Salman Duna
   Ance sunan unguwar ya samo ne daga sunan wata mace mai Suna Salma, mata ga sarkin makera Duna da suka shahara a wajen.
  Wasu sunce wani maharbi mai suna Bono ne ya soma sarar wajen. Shikuma ya kasance miji ne ga zariya ɗiyar sarki Bakwa Turunku.
   Akace wata rana ya fita farauta sai ya riski wurin da ayau ake kira Fadamar Bono, sai ya jima yana farauta har sama da lokacin daya saba idan ya fita gida. Wannan yasa hankalin matarsa ya tashi ta biyo bayansa. 
( Sai akace anan ne har taga yankin Zaria kuma ta kayatu da zama a wurin saboda ni'iamar ruwa da yake dashi, inda daga baya ta roki mahaifinta ya komo da jama'arsa wurin kafin a gama aikin gina gari. Ance jajircewar ta bisa haka yasa ake kiran wajen da sunanta)
  Amma wasu sunce wannan yanki na Salmanduna sanananne tun da jimawa, domin kuwa sarkin zazzau na farko Gunguma ne ya fara sanyawa aka gyara wurin da nufin fara yin noma a yankin. Daga baya mutane suka soma zama har ya zama unguwa.
  Sannan akwai wani yanki mai suna Babban dodo a jikin unguwar Salmanduna, inda akace a baya matattara ce ta bautar iskokai.
Har ma an samu ana yiwa wata iska kirari domin shaida ga bautar da akayi a wurin. Ga kirarin kamar haka:-
  Duna na kar kashin kasa
  Arne Na gidan Nabijari.
Ko uwanka na Tsoronka
Bakaka mushagala
  Mai kallabi da hanjin yaro
  Talaka baya iya ajiyeki
Ko ya ijeki me zai baki
Sai dai ya baki bargon doki.
Ba dai ya baki jini ba.
  Wani mutum a wurin mai suna Mal Mahmud Aliyu, ya faɗa cewar  tun a karni na goma shabiyar  wajen ya haɓaka da jama'a sosai saboda waccan bauta da akeyi, kuma sai a karni na goma sha tara ragiwar mutane a wurin tayi kasa.

LIMAMCIN KONA
  Kamar yadda yazo tun a farko, a tarihin Kona, ance wasu malamai ne da suka zo wucewa ta zazzau tun kafin ayi ginin ganuwa, suna neman inda zasu zauna. Sai babbansu ya kalli wani wajen yace musu "Ko nan zamu zauna? "
   Wasu sun faɗa cewar waɗannan malamai daga wani gari mai suna Kulunfardu suke can kusa da Borno, kuma sun zauna a wani wuri cikin kasar zazzau Inda daga baya ya zamo kauyen kona tun a wajajen shekara ta 1350.
  Don haka da aka gina ganuwa sai suka tashi daga Kona suka shigo zazzau.
An sanyawa  kofar da suka shigo zazzau ta ciki suna Kofar Kona. Sunan Inda suka sauka kuma ya zamo 'Iimancin Kona', domin a lokacin sune malamai masu yin limanci a daular zazzau.
  Haka kuma wannan unguwa ta zamo wurin karantaswa, inda malaman ke koyar da ɗalibai ilimomi na addinin musulunci daga littattafai misalin Bukhari, Jamiu Sagir, Ashafa, Samar-kandi da wasunsu.
   Daga wannan unguwa ne kuma tarihin wasu unguwannin zazzau biyu ya ciro.
  Unguwa ta farko itace Limancin Alfadarai, wadda akace wani balaraben Misra ne ya taɓa zuwa zazzau daga Borno ya sauka a limancin kona. Sunan sa Mal Salihu, kuma a tare dashi akwai alfadarai masu ɗauke da tulin littattafai na addinin musulunci.
   Daga baya sai aka bashi wuri domin ya zauna.
Inda ya koma da zama ake kira da suna limancin Alfadarai zuwa yau, kuma sai daya fifici malaman kona ilimi har ma ya zamo limamin zazzau.
Unguwa ta biyu kuwa itace Limancin Iya.
  Ita kuma akace akwai wani malami kuma limami a Kona wanda ya nemi auren ɗiyar sarkin zazzau.
  Kasancewsr sarkin zazzau na lokacin ɗalibinsa ne wajen neman ilimin addini, sai ya aura masa ita.
  Daga nan sai sarkin ya bashi wurin zama dashi da iyalinsa ya bar kona da zama.
  Unguwar da limamin ya zauna ake kira limancin Iya.

ANGUWAR JUMA
  Ance wannan wuri na daga cikin daɗaɗɗun wurare a birnin zazzau da ake tsammanin tun kafin gina ganuwa akwai mutane a wurin.
  Amma dai abinda aka tafi akai shine, wurin ya haɓaka ne saboda masallacin zazzau na juma'a da aka gina tun karni na goma shabiyar zamanin Sarkin Zazzau Muhammadu Rabbo.
  Don haka akace ainihin sunan Unguwar shine 'unguwar masallacin Juma'a', daga baya mutane suka yanke shi zuwa Unguwar Juma.
  Akwai malaman Juma fulani da suke zaune a wurin. Ance Su jikokin mallam Abubakar ne da akace ya taso daga Futa Toro ya sauka a 'Yandoto, sannan ya zagaya Katsina, kano da Borno har kuma ya sauka a Zaria. 

ANGUWAR ZAGE-ZAGI
Akwai labarai masu saɓani game da tarihin wannan unguwa, amma dai kusan kowa ya yarda cewar asalin unguwar ya samu ne daga wani gida dake wannan unguwa mai suna gidan zage-zagi.
  Wasu suka ce su zage zagi larabawa ne masu yin fatauci da suka sauka a zazzau a karni na goma sha biyar. Sannu a hankali sai auratayya ta haɗasu da hausawa har suka ɓace cikin hausa.
  Akace da kalmar Zak -zak ake kiransu, kalmar data samo asali daga 'Zakkatu', fassarar ta shine takobi da larabci. Ance anji suna yawan cewa 'tazakzaka'  watau karike takobi shiyasa ake ce musu zak-zak, daga baya sunan ya koma zage-zagi.
  Wasu kuma suka ce ai kalmar Zak-zak na nufin tafiya sannu-sannu da larabci.
A Wata ruwayar kuma ance wannan suna na Zage zagi ya samo asali ne daga wani balaraben Fezzan mai suna Usman bn Ismail wanda ya baro gida bayan rigimar data biyo bayan mutuwar mahaifinsa acikin danginsu a wajajen (1786-1806) har kuma ya sauka a zazzau.
  Da saukar sa sai Magajiyar gari ta nemi izinin sarki ta bashi wannan wuri domin ya gina gida ya zauna. Kuma wata korama dake kusa da wajen ake kira Zage zagi.
  Ita koramar ta zamo kamar dandali ne da ake yin bukin al'ada a duk shekara wanda sarki da sauran mutane ke haɗuwa a wurin ana kiɗa da rawa, abinda wasu ke ganin yayi kama da bikin 'gyaran ruwa ' da aka samu anayi a wasu sassan kasar hausa..  
  Amma dai ance a lokacin jihadi mazauna gidan zage zagi basu goyi bayan fulani ba, don haka aka kore su daga gari. Amma daga baya da suka dawo sai aka basu wani matsugunin, aka kuma sauyawa unguwar suna zuwa Unguwar Katuka, amma dai har yanzu ance anfi sanin ta da asalin sunanta.

UNGUWAR KWARBAI
Itace ungjwar bayan gidan sarki.
  Ana ganin sunan ya samo asali ne daga kofar bayan gidan sarki. Watau Kofar Bai.
  Amma wasu sunce sunan daga wasu dakarun sarki ya samo asali waɗanda suka zauna a arewacin unguwar masu suna 'yan kwarbai.

  UNGUWAR MAGAJIYA
Asalin unguwar ance gidan magajiya zaria ne, watau ɗiyar sarkin zazzau Bakwa Turunku.
  Amma daga unguwar aka fitar da Unguwar lalle, Unguwar kaho, da Unguwar magajin aska.

UNGUWAR KUSFA
Shima wannan wuri tsohowar mazauna ce da akace anyi bautar iskokai a ciki tun kafin zuwan musulunci.
  Amma a hankali malamai suka soma zama a wurin.
  Wani mai suna mallam Tankiru akace ya soma zama tare da tulin ɗaliban sa a wurin.
  Daga baya sai mallam Shitu ya maye gurbinsa, wanda ya shahara sosai har ake zuwa daga sassa ɗaukar ilimi gurinsa.
ANAN ZAMU TSAYA DANGANE DA TARIHIN UNGUWANNIN ZAZZAU.

Article Translation in English Language.



SHARE THIS

Author:

I am a blogger by passion and a Website developer by profession, I am currently the CEO of Hausalive.com.ng, a website that brings you a daily needful and useful contents.

0 Comments: