![]() |
Ko kunsan shagalin da a kafi kowane shagali kashe kudi a duniya? to shine shagalin da aka sayi kimanin Abinci ton 18 wato kwatankwacin buhu 360 na abinci da kwalaben giya 25,000 da jiragen sama 100.
Mafi yawan Al'umma zasu yi tunanin cewa irin wannan shagalin ya faru ne a Kasashen irin su Amurka da Ingila da sauran Kasashen turai.
Domin sune a kafi sani da shagulgula irin wannan. To amma zance ba haka yake ba, domin wannan shagalin wanda a kayi ittifakin cewa yafi kowane shagali tsada a duniya ya faru ne a Kasar Iran a lokacin Mulkin tsohon Sarkin Kasar Mohammed Reza Pahlavi wanda a kafi sani da Sarki Shah wanda ya Mulki Kasar Iran daga shekaran 1941 zuwa 1979 lokacin da aka gudanar da juyin juya halin Kasar wanda yakai ga kafa Jumhuriyar Musulunci ta Iran Karkashin Jagorancin mallamin Addinin Kasar Sheikh Ayotollah Ruhollah Khomeini.
Sarki shah ya gudanar da wannan shagalin ne a lokacin bikin murnar cika Kasar ta Iran wacce ake Kira da daular Shah a baya shekaru 2,500 da kafuwa inda ya gudanar da shagalin a persepolis wanda shine babban birnin daular ta shah a wancan lokacin.
A wannan shagalin an yi Kiyasin cewa ya kashe kudi Dalar Amurka kimanin miliyan $300m a wancan lokacin, kwatankwacin Naira Biliyan ₦300 kenan.
A shagalin, an samar da ton na abinci kimanin ton 18 kwatankwacin buhu 360 da kwalaben giya 25,000 da jirage 100, an Samar da dogayen motocin na sarakuna (limousines) guda 600 da motocin alfarma Kiran Mercedez-Benz guda 250 domin dauko manya-manyan baki daga filin jirgin sama zuwa wajen taron wadanda suka zo daga kasashe 65.
A wajen taron Sarki Shah yasa an gina dakunan wucin gadi guda 50 domin manya-manyan baki daga wajen kasar a kusa da ginin kabarin Sarkin Fasha (Iran) na farko, Sarki Cyrus, a kowanne daki a kwai dakin kwana guda biyu da bandaki 2 da wajen kwalliya da babban falo da zai iya daukan Mutane a kalla 12.
A bangaren Abinci da wajen Zama domin cin abincin, Sarki Shah ya samar da Kamfanin girke-gurken abinci na Maxim’s restaurant wanda ke birnin Paris da sauran biranen turai inda Kamfanin ya tafi hutun mako biyu a daukacin biranen turai da yake da rassan shagunan cin Abinci, inda ya umurci daukacin ma'aikatarshi izuwa wajen girke-girken wannan shagali na Sarki Shah.
A Samar da babban teburin cin Abinci domin manya-manyan baki a babban falon taron wanda tsawon shi yakai kimanin 230, mata 125 ne Sarki Shah ya samar domin kawata teburin da kyallaye na alfarma da kayayyakin kwalliya wanda saida suka shafe wata 6 suna aikin.
Tabbas wannan Shagali ne da aka nuna iko da kudi wanda za'a iya kiranshi da almubazzaranci da dukiyar Al'umman Iran wacce a wancan lokacin suke fama da rashin aikin yi da talauchi da karuwan Al'adun turawan yamma.
0 Comments:
Post a Comment