fassarar salatul fatihi

 

Salatul fatihi salatin Annabi ne wanda mabiya darikar tijjaniya suke karantawa a lokutan gudanar da wazifa da sauran ibadu na farilla da nafila domin neman kai gaisuwa da yabo ga fiyayyen halatta Annabi Muhammad (S.A.W).

Fassarar Salatul fatihi

اَللَّهُمَّ صَلِّ عَلى سَيِّدِنَا مُحَمَّدٍ

*ALLAHUMMA SALLI ALA SAYYIDNA MUHAMMAD:

"Ya ALLAH! Kayi Salati Ga Shugabanmu ANNABI

MUHAMMADU S.A.W"

 اَلْفَاتِحِ لِمَا أُغْلِقَ

*AL-FATIHI LIMA UGLIQA:

"Wanda Ya Bude Abinda Yake Boye(Kafin ANNABI

S.A.W Ya Bayyana Komai Yana Cikin Taskar ALLAH Sai Da Ya Zo Ya Bude)"

 وَ اَلْخَاتِمِ لِمَا سَبَقَ

*WAL-KHATIMI LIMA SABAQA:

"Wanda Ya Zama Cikamakin Dukkan Annabawa Da Suka Gaba Ce Shi"

 نَاصِرِ الْحَقِّ بَالْحَقَّ

*NASIRIL HAQQI BIL HAQQI:

"Wato Shi ANNABI (S.A.W), Mai Taimakon Gaskiya

Da Gaskiya Ne,

Qur'ani Yana Cewa:'WA AMINU BIMA NUZILA ALA

MUHAMMADIN WAHUWAL HAQQU"


 وَ الْهَادِي إلى صِرَاطِكَ الْمُسْتَقِيمِ

*WAL HADI ILA SIRADIKAL MUSTAQIM:

"Mai Shiryarwa Zuwa Hanya Madaidaiciya, Haka

ALLAH(S.W.T) Ya Fada Masa:'WA INNAKA LA

TAHDI ILA SIRADIL MUSTAQIM"


 وَ عَلَى آلِهِ حَقَّ قَدْرِهِ و مِقْدَارِهِ الْعَظِيم

*WA ALA ALIHI HAQQA QADRIHI WAMIQDARIHIL'AZIM:

"Ya ALLAH Idan Zaka Masa Salatin Ka Sanya Hadda

Mutanen Gidansa, Kuma Ka Masa Salatin.

Gwargwadon Girmansa a Wajenka, Dama Kai kadai Kasan

Shi, Ka Kuma San Girmansan Nan Dai Wanda Ya Kai

Matuqa"

Wannan Ita Ce SALATUL FATIH Da Wasu Suke Zagi,

Dukkanta Tana Cikin Qur'ani Mai Girma, Kuma

Dukkan Lafuzan Cikinta Daukakar Darajar ANNABI

(S.A.W) ne, Ba Qasqantar Da shi bane, ballantana ku

Qita har ma wasu suna zagin ta,

Allah ya bamu Albarkan Salatil Fatihi Bijahi (S.A.W)



SHARE THIS

Author:

I am a blogger by passion and a Website developer by profession, I am currently the CEO of Hausalive.com.ng, a website that brings you a daily needful and useful contents.

0 Comments: