Liverpool ta cigaba da jan ragamar teburin Premier League bayan ta doke Brentford da ci 4-1

Liverpool ta cigaba da jan ragamar Premier League bayan ta doke Brentford da ci 4-1


Kungiyar Kwallon kafar Liverpool ta cigaba da jan ragamar teburin Premier League na Ingila bayan ta doke Brentford da ci 4-1 a wasan Premier league mako na 25.

dan wasan Liverpool Darwin nunez ne ya fara zura kwallon farko a ragar Brentford din a mintuna 35 da fara wasan bayan nan sai A. Mac Allister ya zura kwallo ta biyu bayan an dawo hutun rabin lokaci da mintuna 10.

Shima Mohamed Salah ya zura tashi Kwallon a mintuna ba 65 kafin dan wasan Brentford din Ivan Toney ya farke mata kwallo daya a mintuna na 75. Cody Gakpo shima ya zura tashi kwallon a ragar Brentford a mintuna na 86 da Fara wasan inda aka tashi Liverpool na da kwallo 4 yayin da Brentford ke da kwallo 1.

Wannan nasaran da liverpool din ta samu ya kara bata daman cigaba da jan ragamar teburin na premier league da maki 57 sai Arsenal dake biye mata mai maki 55.

SHARE THIS

Author:

I am a blogger by passion and a Website developer by profession, I am currently the CEO of Hausalive.com.ng, a website that brings you a daily needful and useful contents.

0 Comments: