Afcon 2023: Shugaban Najeriya, Bola Tinubu zai Kalli wasan karshe na Afcon 2023 tsakanin Najeriya da Cote D'Ivore

Afcon 2023: Shugaban Najeriya, Bola Tinubu zai Kalli wasan karshe na Afcon 2023 tsakanin Najeriya da Cote D'Ivore


Shugaban hukumar Kwallon kafar Afrika CAF, Patrice Motsepe ya sanar da manema labarai cewa Shugaban Najeriya Ahmed Bola Tinubu zai yi tattaki zuwa Abidjan domin Kwallon wasan karshe na cin kofin Kwallon kafar Afrika Afcon 2023 wanda za'a buga tsakanin Najeriya da Ivory Coast ranar Lahadi.

Da yake tattaunawa da manema labarai anyi ma Shugaban hukumar tambayar zuwa yaushe ne Afrika zata sake daukar bakuncin gasar Kwallon kafar duniya, inda ya amsa da cewa Najeriya yakamata ta nema daukar nauyin gasar kuma ya sanar da cewa zai tattauna da Shugaban kasa Bola Tinubu idan yazo game da batun.

Mataimakin Shugaban Najeriya kashim shatima ya halarci wasan kusa da na karshe wanda na najeriyan ta doke Afrika ta kudu da ci 4-2 a bugun daga kai sai mai tsaron gida bayan an tashi wasan 1-1.
Idan ba'a manta ba a tattaunawar da tawagar Super Eagles suka yi da Ministan wasannin ta manhajar zoom sun bukace shi da ya sanar da Shugaban kasa cewa su na bukatan shi yazo Cote D'Ivore domin kallon wasansu, inda kuma ministan yayi Masu alkawarin cewa zai sanar da Shugaban kuma zai zo nan bada jimawa ba.



SHARE THIS

Author:

I am a blogger by passion and a Website developer by profession, I am currently the CEO of Hausalive.com.ng, a website that brings you a daily needful and useful contents.

0 Comments: