Yan Sanda Sun kama wani Matashi dan shekara 17 da laifin damfarar wani mai sana'ar POS

 

'Yan Sanda Sun kama wani Matashi dan shekara 17 da laifin damfarar wani mai sana'ar POS N900,000 a Jigawa
'Yan Sanda Sun kama wani Matashi dan shekara 17 da laifin damfarar wani mai sana'ar POS


'Yan Sanda Sun kama wani Matashi dan shekara 17 bisa zargin damfarar wani mai sana'ar POS N900,000 a karamar hukumar Maigatari a jihar Jigawa.
Mai magana da yawun 'yan sandar Maigatarin, DSP Shiisu Lawal Adam ya sanarwa manema labarai cewa, wani Mai sana'ar POS (injin sana'ar cire kudi) mai suna Aminu Mustapha ya sanar da 'yan Sanda cewa wani matashi yazo domin ya cire kudi a wajensa inda yake sana'ar POS din amma bayan ya bashi injin cire kudin na POS domin ya sanya lambar sirri sai ya damfare shi inda ya tura kudi har N900,000 cikin asusunsu na banki.
bayan ya shigar da korafin ne ga hukumar 'yan sanda, inda aka bi diddigin wanda ake zargi  ake zargin mai suna Tasi'u Adakawa daga karamar hukumar Dala ta jihar kano inda aka kamashi kuma ya amsa zargin da ake yi Masa.
Yan sandar sun sanar da cewa da zaran sun kammala bincike zasu Mika shi kotu domin a gurfanar da shi a gaban Alkali.

SHARE THIS

Author:

I am a blogger by passion and a Website developer by profession, I am currently the CEO of Hausalive.com.ng, a website that brings you a daily needful and useful contents.

0 Comments: