Tawagar Super Eagles ta Najeriya Sun yi Kira ga Shugaban Kasa Tinubu

Tawagar Super Eagles ta Najeriya Sun yi Kira ga Shugaban Kasa Tinubu



Kungiyar Kwallon kafar Super Eagles ta Najeriya sun yi Kira ga Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da cewa kada ya sake kallon wasansu a talabijin, don haka yayi tattaki zuwa Kasar Cote D'Ivoire inda ake gudanar da gasar domin ya nuna goyon bayanshi ga kungiyar Kwallon kafar kasar.
Sun yi wannan Kiran ne a lokacin da tawagar Kwallon kafar kasar suka tattauna da Ministan wasannin Najeriya Sanata John Owan Enoh ta kafar sadarwan Zoom.
Tattaunawar wanda kaftin din kungiyar Ahmed musa ya jagoranta yace "Zamu baka sako ka fada wa Shugaban kasa cewa kada ya sake kallon wasanmu a kafar talabijin, muna so yazo nan ne ya kalle mu domin yayi murna tare da mu".
Ministan ya basu tabbacin cewan "Shugaban zai zo, domin ya fada mani cewa zai zo, don haka fatana shine Allah yasa kungiyar takai matakin da Shugaban zai zo, zan zo maku da Shugaban kasa, ina baku tabbaci" inji Ministan.
Najeriya dai ta samu nasaran zuwa zagayen kifa daya kwala bayan ta yi nasara a wasanni 2 da kunnen doki 1 a rukunin A, inda ta kare a mataki na 2 kasan na 1 Equatorial Guinea. Yanzu Najeriya zata kece raini da tsohuwar abokiyar hamayyarta kuma makwafciyarta kamaru a ranar Asabar 27 ga watan Janairun 2024.


SHARE THIS

Author:

I am a blogger by passion and a Website developer by profession, I am currently the CEO of Hausalive.com.ng, a website that brings you a daily needful and useful contents.

0 Comments: