Gwamnar jiharBorno Kashim Shatima ya baiyana cewa har yanzu Boko haram na iko da kananan hukumomi biyu a jihar Borno wanda hakan ke nuna sabani akan yadda rundunar sojin kasar tayi ikirarin cewa babu wani yanki a halin yanzu da kungiyar ta Boko haram ke mamaye da shi a duk fadin yankin da ke fama da hare-haren kungiyar.
Gwamnan yayi wannan jawabin ne a karshen makon daya gabata lokacin da yake jawabi ga tawagan gwamnatin taraiya karkashin jagorancin Babachir David Lawal, shatima ya shaida masu cewa "a halin yanzu yan kungiyar Boko Haram na iko da kananan hukumomi biyu wadanda suka hada da Abbadam da Mobar sannan kuma suna da tasirin kadan a wasu yankunan Marte.
sai dai shugaban Rundunar sojin Najeriya Lt Gen. Burtain ya musanta jawabin na Gwamna Shatima a lokacin daya ke ma rundunar sojin Najeriya shiyya ta 3 jawabi a birnin Jos, inda yace babu sauran wani yanki a kasar nan da Boko Haram ke iko da shi, ya kuma kara jaddada kudirin da rundunar sojin ta dauka na kawo karken tayar da kayar bayan Kungiyar ta Boko Haram nan da karken wannan shekaran da muke ciki

0 Comments:
Post a Comment