Dattawan gari da iyalan mutanen da aka yi garkuwa da su a Jihar Borno sun yi kira ga Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu da Gwamna Babagana Umara Zulum da su ƙara kaimi wajen ganin an ceto ɗaliban makarantu da sauran mazauna jihar da suka shafe kwanaki 100 a hannun masu garkuwa da mutane.
An gabatar da kiran ne a madadin iyalan wadanda abin ya shafa daga Hawul Askira-Uba Elders Forum, yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a Abuja ranar Juma’a. Kungiyar ta bayyana kwanaki 100 da wadanda aka sace suka shafe a tsare a matsayin lokacin “tsananin firgici, ciwo da wahala” ga iyalansu.
Daga cikin wadanda kungiyar ke neman a ceto akwai ɗalibai 42 na Mussa Primary da Junior Day Secondary School, wadanda rahotanni suka ce an sace su ranar 15 ga Mayu, 2026, a Karamar Hukumar Askira-Uba ta jihar.
Haka kuma, kungiyar ta bukaci a ceto ɗalibai 36 na Government Day Secondary School, Lassa, wadanda aka ruwaito an sace su ranar 29 ga watan Yuni yayin da suke rubuta jarabawar NECO.
Bugu da ƙari, dattawan sun bukaci a ceto mutane 38 da aka ruwaito an sace su a hanyar Buratai zuwa Maiduguri, da sauran mutanen da aka yi garkuwa da su a hanyar Chibok da wasu hanyoyin da ke da hatsari a jihar.
Kungiyar ta jaddada cewa bai kamata a dauki wadanda aka sace a matsayin alkaluma kawai ba, domin kowane mutum da aka yi garkuwa da shi yana da iyali da ke rayuwa cikin fargaba da rashin sanin makomar masoyinsu.
Kungiyar ta roki Shugaba Tinubu, a matsayinsa na babban kwamandan rundunar sojin Najeriya, da ya yi amfani da dukkanin albarkatun tsaron kasa da ake da su wajen ganin an saki yaran da sauran wadanda aka sace.
> “Ya Shugaban Kasa, don Allah ku dawo mana da yaranmu,” in ji kungiyar.
Haka kuma, dattawan sun yi kira ga Gwamna Zulum da ya yi amfani da karfin ofishinsa wajen matsa lamba domin a gaggauta ceto wadanda aka yi garkuwa da su.
Kungiyar ta yi nuni da ceto dalibai da malamansu da aka yi garkuwa da su a Jihar Oyo a matsayin hujjar cewa hadin gwiwar hukumomin tsaro na iya kai ga samun nasarar kubutar da wadanda aka sace.
Yayin da kungiyar ta yaba wa gwamnatin tarayya da jami’an tsaro kan ceto wadanda aka sace a Oyo, ta kuma tambayi dalilin da ya sa ba a nuna irin wannan gaggawa wajen ceto yara da sauran mazauna Borno ba.
Dattawan sun ce ba sa neman fifiko, sai dai a ba mutanen Borno kariya daidai da sauran ‘yan Najeriya, tare da nuna irin wannan gaggawa da kudurin ceto wadanda aka sace.
Sun kuma bukaci hukumomin da abin ya shafa da su rika bai wa iyalan wadanda aka sace sahihan bayanai akai-akai kan kokarin da ake yi na ganin an kubutar da ‘yan uwansu.

0 $type={blogger}:
Post a Comment