An Kashe Mutane Uku, Yayin Da Bakwai Suka Jikkata A Harin Bindiga Da Aka Kai Wani Gidan Abinci A Jihar Idaho na Amurka.

An Kashe Mutane Uku, Yayin Da Bakwai Suka Jikkata A Harin Bindiga Da Aka Kai Wani Gidan Abinci A Jihar  Idaho na Amurka.

Aƙalla Mutane uku ne suka rasa rayukansu, yayin da wasu bakwai suka jikkata sakamakon harbin bindiga da ya auku a gidan abinci na In-N-Out Burger da ke birnin Twin Falls na jihar Idaho ta Amurka, a ranar Asabar.

Jami'an 'yan sanda sun bayyana cewa sun gano gawar wanda ake zargin ya kai harin a kusa da gidan abincin. Sai dai har yanzu ba a tabbatar ko an ƙirga shi cikin adadin waɗanda suka mutu ba.

Babban Jami'in 'Yan Sandan Twin Falls, Matthew Hicks, ya ce ana ci gaba da bincike domin gano ainihin wanda ya kai harin da kuma dalilin aikata shi. Ya kuma tabbatar da cewa babu sauran barazana ga al'umma.

Wasu daga cikin waɗanda suka jikkata na ci gaba da samun kulawa ta musamman a asibiti saboda munin raunukan da suka samu. Hukumomi ba su bayyana sunayen waɗanda abin ya shafa ba, domin ana ci gaba da sanar da iyalansu.

Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 2:00 na rana agogon yankin, a sabon gidan abinci na In-N-Out Burger da aka buɗe kwanan nan a ranar 24 ga watan Yuli.

Shaidun gani da ido sun ce mutane sun rika gudu cikin firgici yayin da aka fara harbe-harbe. Wasu ma'aikatan gidan abincin sun taimaka wajen fitar da waɗanda suka jikkata zuwa wurare masu aminci kafin jami'an agajin gaggawa su isa.

An garzaya da waɗanda suka jikkata zuwa Asibitin St. Luke's Magic Valley Medical Center domin samun kulawa, yayin da 'yan sanda ke ci gaba da tattara shaidu da gudanar da bincike kan lamarin.

0 $type={blogger}: