Rundunar Sojin Najeriya Ta Karrama Jami'anta Da Suka Jikkata a jihar Borno A Ranar Sojojin ta 2026.

Rundunar Sojin Najeriya Ta Karrama Jami'anta Da Suka Jikkata a jihar Borno A Ranar Sojojin ta 2026.

Rundunar Sojin Najeriya ta shirya liyafa ta musamman domin karrama jami'an sojin da suka jikkata yayin fafatawa da 'yan ta'adda a Arewa maso Gabashin kasar nan, a wani bangare na bikin Ranar Sojojin Najeriya ta 2026.

An gudanar da taron ne a Asibitin Runduna ta 7 da ke Maimalari Cantonment, Maiduguri, Jihar Borno.

Da yake jawabi a wajen taron, Kwamandan Operation Hadin Kai, Manjo Janar Abdulsalam Abubakar, wanda Mataimakinsa Air Vice Marshal Olushola Akinboyewa ya wakilta, ya yaba da jarumtaka da sadaukarwar dakarun da suka jikkata. Ya ce duk wata nasarar da rundunar ta samu a yaki da ta'addanci ta samo asali ne daga jajircewa da sadaukarwar sojojin Najeriya.

Ya bayyana cewa raunukan da dakarun suka samu ba alamar rauni ba ne, illa shaidar jarumtaka da biyayya ga kasa wajen kare rayuka da dukiyoyin al'umma.

Haka kuma, ya karrama sojojin da suka rasa rayukansu a fagen fama, yana mai tabbatar da cewa rundunar ba za ta taba mantawa da sadaukarwarsu da kuma kula da iyalansu ba.

Ya kuma yabawa likitoci, ma'aikatan jinya da sauran jami'an lafiya saboda kokarinsu wajen kula da dakarun da suka jikkata, tare da gode wa iyalansu bisa hakuri da goyon bayan da suke ba su.

A nasa jawabin, Mukaddashin Babban Kwamandan Runduna ta 7, Birgediya Janar Solomon Diwa, ya ce raunukan da dakarun suka samu alamu ne na jarumtaka da sadaukarwa wajen kare Najeriya.

Ya tabbatar wa dakarun da suka jikkata cewa jin dadinsu da kula da lafiyarsu na daga cikin manyan abubuwan da Rundunar Sojin Najeriya ta sanya a gaba, tare da alkawarin ci gaba da ba su ingantacciyar kulawar lafiya da tallafin farfadowa.

An shirya wannan liyafa ne domin girmama sadaukarwar dakarun da suka jikkata tare da nuna cewa Rundunar Sojin Najeriya na ci gaba da tsayawa tare da su bayan hidimarsu a fagen daga.

0 $type={blogger}: