Mutane 600 ne kacal daga cikin 8,000 suka yi nasara a tantancewar daukar malamai a jihar Nasarawa – inji Gwamnatin jihar.

Mutane 600 ne kacal daga cikin 8,000 suka yi nasara a tantancewar daukar malamai a jihar Nasarawa – inji Gwamnatin jihar.

Gwamnatin Jihar Nasarawa ta bayyana cewa malamai 600 kacal ne daga cikin mutane 8,000 da suka halarci jarabawar tantancewa suka yi nasara a shirin daukar sabbin malaman karkara 1,000 da gwamnatin jihar ke son dauka.

Mai Bai wa Gwamna Shawara na Musamman kan Harkokin Jama'a, Peter Ahemba, ne ya bayyana hakan yayin taron manema labarai da ake gudanarwa duk bayan wata biyu a jihar.

A cewarsa, Hukumar Ilimin Bai Daya ta Jihar Nasarawa (SUBEB) ta samu kimanin masu neman aikin su 10,000, yayin da mutane 8,000 suka rubuta jarabawar tantancewar, amma 600 ne kawai suka samu nasara, adadin da bai kai yawan malaman da gwamnati ke bukata ba.

Ahemba ya ce kamfanin da aka ba aikin gudanar da tantancewar ya kammala aikinsa tare da mika sakamakon ga SUBEB domin ci gaba da sauran matakan daukar aikin.

Ya kuma gargadi masu yaudarar jama'a da ke karbar kudade suna alkawarin samar wa mutane aiki ta bayan fage, yana mai cewa gwamnati ba za ta lamunci duk wata magudi ko cin hanci a wannan aikin daukar malamai ba.

> “Ba za a ba wa wata almundahana ko magudi dama ba a wannan aikin daukar malamai. Za a dauki wadanda suka cancanta ne kawai,” in ji shi.

Ya kara da cewa duk malaman da za a dauka za a tura su ne zuwa yankunan karkara domin rage karancin malamai a makarantun firamare na kauyuka.

A wani bangare kuma, gwamnatin jihar ta amince da gina manyan gine-ginen ajujuwa masu hawa uku a shiyyoyin sanata uku na jihar wato Keffi da Akwanga da Lafia.

Haka kuma ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta amince da gina makarantun zamani (Model Schools) a kowace shiyyar sanata ta jihar domin yabawa kokarin gwamnatin Nasarawa wajen inganta ilimin bai daya.

Wannan na nuna cewa kusan kashi 7.5% ne kawai na wadanda suka rubuta jarabawar suka samu nasara.

0 $type={blogger}: