Gwamnatin Tarayya ta sanar da cewa rukuni na ƙarshe na 'yan Najeriya su 315 da ake kwaso wa daga Afirka ta Kudu za su iso Najeriya a ranar Laraba, 15 ga Yuli, 2026.
Ma'aikatar Harkokin Wajen Ƙasa ta bayyana cewa jirgin Air Peace na biyar kuma na ƙarshe zai tashi daga Johannesburg da misalin ƙarfe 1:30 na dare, sannan ana sa ran zai sauka a Filin Jirgin Sama na Murtala Muhammed da ke Legas da misalin ƙarfe 6:30 na safe.
An shirya wannan aikin dawo da 'yan ƙasar ne domin taimaka wa 'yan Najeriya da suka nuna sha'awar komawa gida bayan hare-haren ƙyamar baƙi da matsalolin tsaro da suka faru a wasu sassan Afirka ta Kudu.
Gwamnatin Tarayya ta ce tun bayan fara aikin dawo da 'yan ƙasar a ranar 11 ga Yuni, 2026, jirage huɗu sun riga sun dawo da 'yan Najeriya 1,141 gida.
Haka kuma, Wani mutum mai zaman kansa ya taimaka wajen dawo da mutane 66, yayin da Kamfanin Air Peace ta shirya dawowar wasu mutum 39.
Ma'aikatar Harkokin Wajen Ƙasar ta sake jaddada kudirin Gwamnatin Tarayya na kare lafiya da jin daɗin 'yan Najeriya a duk inda suke a duniya, tare da gode wa Kamfanin Air Peace da sauran masu ruwa da tsaki da suka ba da gudummawa wajen nasarar wannan shiri.

0 $type={blogger}:
Post a Comment