Jihar Kano Za Ta Kaddamar da Kamfanin Jirgin Sama mallakin Jihar Cikin Shekara Daya.

Jihar Kano Za Ta Kaddamar da Kamfanin Jirgin Sama mallakin Jihar Cikin Shekara Daya.

Gwamnatin Jihar Kano ta sanar da shirinta na kafa kamfanin jirgin saman mallakar jihar domin samar da guraben aikin yi ga matukan jirgi 'yan asalin jihar da suka kammala horon aikin tukin jirgin sama.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya bayyana hakan yayin taron Majalisar Zartarwa ta Jiha karo na 40 da aka gudanar a Fadar Gwamnatin Kano, inda kuma aka karrama shi da lambobin yabo daban-daban, ciki har da na Kungiyar Matuka Jiragen Sama ta Jihar Kano.

Gwamnan ya ce ana sa ran sabon kamfanin jirgin saman, wanda za a sanya wa suna Kano Airline, zai fara aiki cikin shekara guda mai zuwa.

Ya bayyana cewa gwamnatin jihar za ta samar da dukkan goyon bayan da ake bukata domin tabbatar da nasarar wannan shiri.

Har ila yau, Gwamna Yusuf ya yabawa matukan jiragen saman da gwamnatin Kano ta dauki nauyin horas da su a kasar Jordan, yana mai cewa sun nuna kwarewa da hazaka, kuma gwamnati za ta ci gaba da tallafa musu domin su ba da gudummawa ga ci gaban harkokin sufurin jiragen sama.

A nasa jawabin, Shugaban Kungiyar Matuka Jiragen Sama ta Jihar Kano, Naziru Ibrahim, ya gode wa gwamnan bisa taimakon da ya bayar wajen sabunta lasisin tuka jirgin sama na mambobin kungiyar.

Ya kuma roki gwamnatin jihar da ta ci gaba da tallafa musu domin su samu takardun shaidar karshe da za su ba su damar gudanar da zirga-zirgar jiragen kasuwanci a Najeriya da ma kasashen waje.

Ana sa ran kafa kamfanin jirgin saman zai bunkasa harkokin sufurin jiragen sama a jihar da samar da ayyukan yi ga matasa, tare da kara habaka tattalin arzikin Kano.

0 $type={blogger}: