Wasu karin ‘yan Najeriya 271 da aka kwashe daga Afirka ta Kudu sun isa Legas a ranar Talata, a karkashin shirin gwamnatin tarayya na mayar da ‘yan Najeriya gida bisa radin kansu.
Jirgin kamfanin Air Peace ya sauka a Filin Jirgin Sama na Murtala Muhammed da ke Legas jim kadan kafin karfe 11 na safe, bayan ya tashi daga Johannesburg da misalin karfe 5 na safe agogon wurin.
Jami’ai daga Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA), Hukumar Shige da Fice ta Najeriya, da Hukumar Kula da ‘Yan Najeriya a Kasashen Waje (NiDCOM) ne suka tarbi wadanda suka dawo.
Wannan kwashewar wani bangare ne na kokarin gwamnatin tarayya na taimaka wa ‘yan Najeriya da suka zabi komawa gida sakamakon karuwar rikicin nuna kyamar bakin haure a Afirka ta Kudu.
Dawowar nasu na zuwa ne gabanin wa’adin ranar 30 ga watan Yuni da wasu kungiyoyin sa-kai da masu fafutuka suka bayar, inda suke neman bakin hauren da ba su da takardu su bar kasar.
A farkon wannan watan, Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya amince da shirin mayar da ‘yan Najeriya gida bisa radin kansu. Ma’aikatar Harkokin Wajen Najeriya ta kuma ce an amince da jiragen Air Peace biyar domin kwashe wadanda suka yi rajista.
Kafin wannan jirgin na ranar Talata, an riga an kwashe ‘yan Najeriya 328 cikin rukuni biyu — 262 sun dawo ranar 11 ga Yuni, yayin da 66 suka dawo ranar 25 ga Yuni.
Mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Waje, Kimiebi Ebienfa, ya ce jirgin na baya-bayan nan ya dawo da ‘yan Najeriya 271 da suka nuna sha’awar komawa gida. Ya kuma ce akwai yiwuwar a kwashe wasu karin 700 bisa la’akari da halin da ake ciki a Afirka ta Kudu.
A halin yanzu, an kara tsaro a wasu sassan Afirka ta Kudu yayin da ‘yan sanda ke sa ido kan zanga-zangar adawa da bakin haure a manyan birane.
A Johannesburg, wasu kasuwanni sun kasance a rufe yayin da jami’an tsaro suka bazu a wurare daban-daban. Kungiyoyin siyasa da wasu masu fafutuka ne suka shirya zanga-zangar suna neman bakin hauren da ba su da takardu su bar kasar.
A Durban kuma, wasu masu zanga-zanga sanye da kayan gargajiya na Zulu sun taru a wani fili suna rera wakar “Abahambe” (Su tafi), yayin da jami’an tsaro ke bibiyar lamarin.

0 $type={blogger}:
Post a Comment