‘Yan Bindiga Sun Kashe Shugaban Miyetti Allah na jihar Benue da Wani Mutum.

‘Yan Bindiga Sun Kashe Shugaban Miyetti Allah na jihar Benue da Wani Mutum.

Wasu ‘yan bindiga sun kashe shugaban ƙungiyar Miyetti Allah (Ƙungiyar Makiyaya Masu Kiwo ta Najeriya, MACBAN) na Jihar Benue, Ardo Muhammad, tare da wani mutum mai suna Yakubu Isah.

An ce lamarin ya faru ne a ƙaramar hukumar Otukpo ta Jihar Benue, lamarin da ya haifar da zaman dar-dar a Otukpo da yankunan da ke kusa.

Rahotanni sun bayyana cewa Ardo Muhammad ya halarci wani taron sulhu da jami’in ‘yan sanda na yankin Ohinmini ya shirya tare da shugabannin al’ummar Ayunne domin sasanta rikicin da ya faru a baya.

Bayan kammala taron, yayin da suke kan hanyar komawa gida, wasu ‘yan bindiga sun yi wa motarsu kwanton ɓauna a yankin Okudu da ke Otukpo, inda suka kashe shi da abokin tafiyarsa.

Ɗan marigayin ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce an yi wa mahaifinsa kwanton ɓauna kafin a kashe shi.

Shugaban ƙaramar hukumar Otukpo, Maxwell Ogiri, ya tabbatar da kisan, yana mai cewa lamarin ya haifar da tashin hankali a yankin.

Ya kuma yi kira ga jama’a da su zauna lafiya yayin da jami’an tsaro ke ƙoƙarin shawo kan lamarin.

Kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar Benue, DSP Udeme Edet, ta ce sun samu rahoton harin kuma an fara gudanar da bincike.

Al’ummomin Otukpo da Ohinmini sun sha fama da hare-hare daga wasu da ake zargi da ɗauke da makamai a baya.

0 $type={blogger}: