Yawan Mutanen Da Suka Mutu A Girgizar Ƙasa A Venezuela Ya Zarce Mutane 900 Yayin Da Ake Ci Gaba Da Aikin Ceto.

Yawan Mutanen Da Suka Mutu A Girgizar Ƙasa A Venezuela Ya Zarce Mutane 900 Yayin Da Ake Ci Gaba Da Aikin Ceto.

Ƙungiyoyin ceto suna fafutukar neman waɗanda suka tsira bayan girgizar ƙasa guda biyu da suka afku a Venezuela, lamarin da ya yi sanadin mutuwar sama da mutane 900 tare da jikkata dubbai.

Mahukunta sun bayyana cewa aƙalla mutane 920 ne suka mutu, yayin da fiye da 3,300 suka ji rauni sakamakon girgizar ƙasar mai muni da ta shafi yankuna da suka haɗa da Caracas da La Guaira. 
Mutane da dama har yanzu suna makale a ƙarƙashin rusassun gine-gine, yayin da jami’an ceto ke ci gaba da bincike.

Jami’ai sun ce ana kyautata zaton akwai akalla mutane 172 da har yanzu suke ƙarƙashin baraguzan gine-gine, yayin da masu ceto ke amfani da sa’o’in farko na awanni 72 da ake ganin sun fi dacewa wajen gano wadanda suke raye.

Girgizar ƙasar ta haifar da babbar barna, inda daruruwan gine-gine suka lalace. A La Guaira, daya daga cikin wuraren da abin ya fi shafa, mazauna yankin sun bayyana cewa wurin ya koma kamar “filin yaƙi.”

Taimakon ƙasa da ƙasa ya fara isa Venezuela, inda ƙasashe ciki har da Amurka da Colombia da Mexico da Spain suka tura jami’an ceto da ma’aikatan lafiya da kayan aiki da tallafin gaggawa.

Sai dai aikin ceton na fuskantar matsaloli da suka haɗa da lalacewar hanyoyi da gine-gine da ci gaba da ƙananan girgizar ƙasa, da ƙarancin manyan injuna. 
Wasu mazauna yankin sun yi kira da a ƙara yawan masu aikin sa kai domin taimakawa wajen cire baraguzan gine-gine.

Tsarin kiwon lafiya na Venezuela, wanda ya sha fama da matsalolin ƙarancin kayan aiki da matsin tattalin arziki, na fama da ƙalubalen kula da yawan waɗanda suka jikkata. 
Likitoci sun yi gargadin cewa asibitoci na fuskantar ƙarancin muhimman magunguna da kayan aiki.

Ƙungiyoyin agaji sun ce aikin farfadowa zai iya ɗaukar watanni, yayin da iyalai da dama suka rasa gidajensu kuma suke buƙatar abinci da ruwa da tallafin lafiya.

Mahukunta sun shawarci jama’a da su nisanci wuraren da suka fi lalacewa domin bai wa jami’an ceto damar kai taimako da jigilar waɗanda suka jikkata cikin sauƙi.

0 $type={blogger}: