Rundunar Sojojin Najeriya Za Su Dauki Sabbin Sojoji 28,000 Domin Yaki da Matsalolin Tsaro.

Rundunar Sojojin Najeriya Za Su Dauki Sabbin Sojoji 28,000 Domin Yaki da Matsalolin Tsaro.

Rundunar Sojojin Najeriya ta bayyana shirin daukar sabbin sojoji 28,000 domin kara karfin dakaru da kuma fuskantar matsalolin tsaro da ke kara ta’azzara a fadin kasar.

Shugaban Hafsoshin Sojojin Najeriya, Laftanar Janar Waidi Shaibu, ya bayyana cewa wannan shiri ya biyo bayan kafa sabuwar cibiyar horas da sojoji a Amasiri-Edda, Afikpo da kuma kananan hukumomin Edda da ke jihar Ebonyi.

Rundunar ta ce matakin zai taimaka wajen kara yawan dakaru da inganta karfin yakar barazanar tsaro kamar ta’addanci da garkuwa da mutane da ‘yan bindiga da kungiyoyin ballewa da sauran matsalolin da ke barazana ga zaman lafiyar kasa.

A yayin wani taron manema labarai gabanin bikin Ranar Sojojin Najeriya ta shekarar 2026, rundunar ta ce tana gudanar da sauye-sauye da suka hada da kafa sabbin rundunoni da samar da kayayyakin yaki na zamani da inganta gine-gine da kuma kula da jin dadin sojoji.

Taken bikin na bana shi ne: “Kare Kasa da Bautawa Jama’a: Hanyar Ci Gaban Sojojin Najeriya.”

Sojojin sun sake jaddada cewa za su ci gaba da kare iyakokin Najeriya tare da taimakawa hukumomin farar hula wajen tabbatar da doka da oda.

Ana sa ran daukar sabbin sojojin zai kara karfin rundunar wajen yaki da matsalolin tsaro a sassan Najeriya.

0 $type={blogger}: