Gwamnatin Burkina Faso ta sanar da cewa ta yanke hulɗar diflomasiyya da Faransa a hukumance, matakin da ya ƙara janyo tsamin dangantaka tsakanin ƙasar da tsohuwar mai mulkinta.
Sanarwar ta zo ne bayan shekaru da dama ana samun ƙarin rashin jituwa tsakanin ƙasashen biyu kan batutuwan tsaro da ikon ƙasa da kuma zargin katsalandan daga waje.
Burkina Faso na fama da hare-haren ƙungiyoyin masu tayar da ƙayar baya da ake zargi da alaƙa da masu tsattsauran ra'ayi, lamarin da ya yi sanadin mutuwar dubban mutane tare da raba miliyoyin jama'a da muhallansu a cikin shekaru fiye da goma da suka gabata.
Ministan Yaɗa Labarai na Burkina Faso, Gilbert Ouedraogo, ya ce matakin ya fara aiki ne a ranar 26 ga watan Yuni bayan gwamnati ta sake duba dangantakarta da Paris.
Ya bayyana cewa ba a sake samun muhimman sharuddan da za su ba da damar ci gaba da hulɗa bisa mutunta juna da amincewa da juna da rashin tsoma baki cikin harkokin cikin gida da kuma mutunta ikon ƙasar ba.
Ministan ya kuma zargi Faransa da goyon bayan “ƙungiyoyin da ke tayar da zaune tsaye” da kuma “’yan ta’adda,” zargin da Faransa ta taɓa musantawa a baya.
Wannan mataki ya ƙara nuna yadda Burkina Faso ke ƙara nesanta kanta daga Faransa, yayin da take neman sabbin ƙawance da kuma ƙara samun ‘yancin kai a harkokin tsaro da manufofin ƙasashen waje.

0 $type={blogger}:
Post a Comment