Harin Isra’ila a kan wata mota a tsakiyar zirin gaza yayi sanadin mutuwar falasɗinawa uku.

Harin Isra’ila a kan wata mota a tsakiyar zirin gaza yayi sanadin mutuwar falasɗinawa uku.

Wani hari da Isra’ila ta kai kan wata mota a tsakiyar Zirin Gaza ya yi sanadiyyar mutuwar Falasɗinawa uku tare da jikkata wasu mutane.

Ma’aikatar Cikin Gida da Tsaron Ƙasa ta Falasɗinu ta ce harin ya faru ne a kusa da ƙofar sansanin ‘yan gudun hijira na Maghazi da ke Deir el-Balah ranar Juma’a, inda ta bayyana cewa duk waɗanda aka kashe jami’an ‘yan sanda ne.

Ma’aikatar ta bayyana sunayen waɗanda suka mutu da Kyaftin Mansour Sami Shahtout da Kyaftin Mohammed Khaled Nofal da Sajan Mahdi Nader Jabr.

Kamfanin dillancin labarai na Wafa ya ruwaito cewa jirgi mara matuƙi na Isra’ila ne ya kai hari kan motar, inda aka ce an harba makamai masu linzami akalla biyu wanda ya sa motar ta kama da wuta.

Shaidun gani da ido sun ce an kai harin ne a kan titin Salah al-Din kusa da ƙofar sansanin Maghazi. Jami’an agaji, masu kashe gobara da ma’aikatan lafiya sun isa wurin lokacin da abun ya faru, domin gudanar da aikin ceto.

An kai gawarwakin waɗanda suka mutu zuwa asibitin Al-Aqsa Martyrs da ke Deir el-Balah.

Ma’aikatar Cikin Gida ta Falasɗinu ta yi Allah-wadai da harin, tana mai cewa ya karya yarjejeniyar tsagaita bude wuta tare da zargin Isra’ila da ci gaba da kai hare-hare kan jami’an tsaro a Gaza.

An fara aiwatar da yarjejeniyar tsagaita bude wuta a Gaza tun watan Oktoban 2025, amma rahotanni sun ce ana ci gaba da samun take hakkokinta, inda hare-haren Israi'la suka yi sanadiyyar mutuwar Falasɗinawa da dama tare da jikkata dubban wasu.

A gefe guda kuma, Hamas ta ce tana ci gaba da tattaunawa da sauran ƙungiyoyin Falasɗinawa da masu shiga tsakani domin tabbatar da cikakken aiwatar da yarjejeniyar tsagaita bude wutar.

0 $type={blogger}: