Mataimakin Shugaban Amurka, J.D. Vance, ya isa ƙasar Switzerland a ranar Lahadi domin gudanar da tattaunawa da jami’an Iran kan neman hanyar warware rikicin da ke tsakanin bangarorin cikin lumana.
Vance da matarsa sun sauka a sansanin jiragen sama na Emmen da ke Switzerland da sassafe, kamar yadda mai magana da yawun mataimakin shugaban kasar ya bayyana.
Vance ya ce tattaunawar da jami’an Iran za ta iya daukar kwanaki da dama, yayin da bangarorin biyu ke kokarin samun mafita ta hanyar diflomasiyya.
Ana sa ran tattaunawar za ta mayar da hankali kan batutuwan tsaro a yankin, ciki har da rikicin da ya shafi mashigar ruwan Hormuz da kuma dangantakar Amurka da Iran.

0 $type={blogger}:
Post a Comment